– Kasar Singapore ta aika da wani dan Nigeria lahira ta hanyar rataya duk da kiraye-kirayen a yi mi shi afuwa
– Kungiyar Amnesty International ta yi rokon a da mayar da hukuncinsa daurin rai-da-rai, amma kasara ta ki
Gwamnatin Singapore ta aiwatar da hukuncin kisa kan Chijioke Stephen Obioha wani Nigeria da aka kama da laifin safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar.
An dai aiwatar da hukuncin kisan ne kan Chijioke a safiyar ranar Juma’a 18 ga watan Nuwamba, shi da wani dan kasar Malaysia mai suna Devendran A/L Supramaniam, duk da kiraye-kirayen a yi musu afuwa.
An dai kama Obioha ne da tabar wiwi mai nauyin sama da kilogiram miliyan biyu, wanda ya wuce ka’idar hukuma na giram 500, a bisa dokar kasar ta 2007 kan haramcin kwayoyi, wanda hakan tamkar safara ne.
An ce Chijioke na kasar Singapore ne tun shekarar 2005 a bisa dalilin neman buga kwallon kafa, amma jami’an yaki da miyagun kwayoyi suka kama shi.
Dan shekara 31, Chijioke wanda ya yi karantunsa na digiri a jami’ar Benin a fannin kimiyyar harhada magunguna, an same shi da makullan wani daki da aka boye wasu haramtattun abubuwa, wanda haka ya sa mahukunta su yi ram da shi, da kuma ayyana cewa, yana safarar miyagun kwayoyi zuwa kasar.
Kungiyar Amnesty International ta yi kira da a yi masa afuwa, ta na mai togaciya da cewa, laifin da ake tuhumarsa bai fada karkashin muggan laifuka ba, amma gwamnatin kasar wacce ke da tsatsauran dokoki kan miyagun kwayoyi ta yi watsi da rokon.
Lauya mai kare shi, ya shigar da rokon dakatar da aiwatar da hukuncin, da kuma neman da a mayar da hukuncin zuwa daurin rai-da-rai, a ranar Alhamis 16 ga watan Nuwamba, amma kotu ta yi watsi da rokon.
https://www.youtube.com/watch?v=t9jMQKyVAW4&t=2s
The post Singapore ta rataye dan Nigeria bisa wannan dalili appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Originally posted by Adeshola