Breaking News
Loading...

Abun Murna: Buhari ya bayar da umurnin cigaba da binciken mai a arewa

Abun Murna: Buhari ya bayar da umurnin cigaba da binciken mai a arewa

– A Najeriya, kamfanin man kasar, wato NNPC ya sake komawa yankin Chadi don ci gaba da bincike da nufin gano ainihin adadin mai da iskar gas din da ke karkashin kasa a yankin

– A wata hira da majiyar mu, shugaban kamfanin man Najeriya, Dr Maikanti Baru, ya ce NNPC zai yi amfani da wasu manyan na’urori wajen yin binciken

buhari-and-NNPC

Ya kara da cewa idan har abun da aka samu ya kai wani mizani, to kamfanin zai dukufa wajen hakar man.

Tun a shekarun 1970 ne wasu masana da kuma kamfanin NNPC suka yi hasashen cewa za a iya samun mai a yankin, kuma tun daga wancan lokacin aka yi yunkuri daban-daban don binciken man amma ana dakatarwa saboda wasu dalilai, ciki har da zargin cewa akwai siyasa a cikin lamarin.

KU KARANTA: Kamfanin Glo na shirin fuskantar fushin gwamnatin Katsina

A wani labarin makamancin wannan dai, a watan jiya ne Najeriya ta roki Amurka da ta dage matakin daina sayen danyen man fetur dinta, tana mai cewa matakin bai dace da tsarin bunkasar kasuwanci da mu’amullar tattalin arziki ba.

Ministan kwadago da ayyuka, na Najeriyar, Sanata Chris Ngige, ya yi rokon a birnin Washington na Amurka yayin taron ministoci kan shirin bunkasar Afrika (AGOA) da samar da dama, a ma’aikatar kwadago ta Amurka.

Ngige ya ce daina sayen man da Amurka ta yi, ya sa kudaden da Najeriya ke samu ya ragu kuma hakan ya shafi hatta wasu kasashen Afrika.

Ministan ya ce sauya wannan shawara ta Amurka a kan Najeriy na daya daga matakan da za su taimaka wa Najeriyar ta iya kare ‘yanci da hakkin ma’aikata.

Raguwar kudaden wajen na Najeriya kuma ya sa tana kasa aiwatar da wasu ka’idoji na kwadago, kamar hana yara shiga ayyukan kwadago da safarar dan adam da ci da biyan ma’aikata albashi dan kadan.

Dakta Ngige ya bukaci Amurka ta taimaka wa kasashen Afurka tattalin arzikinsu ya bunkasa ta fannin aikin gona, a hanyoyin ilmantar da manoma

The post Abun Murna: Buhari ya bayar da umurnin cigaba da binciken mai a arewa appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Originally posted by Adeshola
Share on Google Plus

About Unknown

This is a short description in the author block about the author. You edit it by entering text in the "Biographical Info" field in the user admin panel.