– Mayakan kungiyar Boko Haram sun kai hari a wasu kauyukan da ke karamar hukumar Monguno a jahar Borno inda suka hallaka mutane 22
– Rahotanni da ke fitowa daga kasar na cewa an kai harin ne tun ranakun litinin da talata amman sai yau labarin harin ke fitowa
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Najeriya ke cewa, ta na tattaunawa da wakilan kungiyar don sako ‘yan matan sakandaren Chibok fiye da dari biyu da Boko Haram din ta sace a shekarar 2014.
Munguno na daga cikin garuruwan jahar Borno da Boko Haram ta kwace kafin sojin Najeriya su sake kwato ta daga kungiyar.
KU KARANTA: Gwamnatin tarayya ta roki malaman jami’oi kan yajin aiki
Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da dubu dari biyu.
A wani labarin kuma, Rundunar hadin gwiwa na ta kasashen yankin tafkin Chadi ta ce daruruwan mayakan Boko Haram ne suka mika wuya, yayin da ake ci gaba da samun karuwar hare haren a bangaren Najeriya.
A wata sanarwa da ya aikawa manema labaru kakakin hedikwatar dakarun kasashen yankin tafkin Chadi Kanal Mohammed Dole, yace daruruwan mayakan Boko Haram sun ajiye makamansu suka mika kai. Kara tsawwala matakan da ake dauka akansu shine ke dalilin fitowar mayakan suna mika wuya, yanzu dai akwai mayaka 240 da suka riga suka mika wuya.
Yayin da a bangaren Chadi mayakan ke mika wuya sai gashi a bangaren Najeriya sai ‘kara kai hare hare suke yi, a cewar Mohammed Dole hakan na faruwa ne a duk lokacin da aka bude musu wuta a wani bangare sai su gudu zuwa wani bangare.
Dakta Bawa Abdullahi Wase, na ganin girman filin kasa ne ke haddasawa mayakan dake yankin tafkin Chadi mika wuya, kasancwar sojojin hadin gwiwa sun bude musu wuta babu yadda zasuyi wajen sake komawa wani bangaren.
The post Mayakan Boko Haram sun sake wani mummunan hari tare da hallaka mutane 22 appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Originally posted by Adeshola