Breaking News
Loading...

Bahallatsar $2.1b: Shaidu sun saka Fayose cikin tsaka mai wuya

Bahallatsar $2.1b: Shaidu sun saka Fayose cikin tsaka mai wuya

Da alama gwamna Fayose na cikin tsaka mai wuya yayin da shaidun lauya mai kara suke yi mai tonan silili kan shari’ar badakalar $2.1b dake gudana.

Fayose

Shaidu na kara daure gwamna Fayose cikin wannan shari’ar wanda ta samo asali daga yadda aka yi waka-ci wa-tashi da kudaden al’umma daga ofishin tsohon mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro kanal Sambo Dasuki mai murabus.

Shaidan masu kara, Alade Sunday wanda jami’i ne a wani banki dake da reshe a garin Akure, jihar Ondo. Alade ya bayyana cewar shi ya aika da Naira miliyan 2.5 zuwa asusun bankin Gwamna Fayose a ranar 11 ga watan Yuni, sa’annan ya sake aika masa Naira miliyan 90 a ranar 23 ga watan Yuni na 2014.

Alade ya bayyana haka ne a ranar Alhamis 17 ga watan Nuwamba a gaban alkali Nnamdi Dimgba yayin da ake shari’ar Biodun Agbele wanda aminin Gwamna Fayose ne.

KU KARANTA: Hotunan Samira, yarinyar minista Amina Muhammed

Yayin da da lauyan wanda ake kara Mike Ozekhome yake yi ma Alade tambayoyi, Alade yace ya tura ma Gwamna Fashola Naira miliyan 1a ranar 2 ga watan Yuni, inda ya kara sanya masa N895,315 a ranar 5 ga watan Yuni 2014.

Sai dai Alade ya gamsu da zancen cewar asusun ya dade yana aiki tun kafin Gwamna Fayose ya zama Gwamna.

“A cikin jakar Ghana Must Go na zuba kudaden gwamna Fayose, inda muka kai masa a cikin jiragen sama guda biyu. Mintuna 45 muka kwashe muna sauke jakkunan daga jiragen tare da taimakon Olaolu Omotosho da wani wasu masu gadi dasu ka rako Agbele.

“bayan mun gama tattaunawa da tsohon ministan tsaro Musliu Obanikoro a filin tashin jirgi, sai wani mutum mai suna Adewale A.O wanda yace shine hadimin Obanikoro ya raka mu, sai dai Agbele ya bukaci dole ne a kirga kudaden. “bayan mun kammala kirga kudaden ne, sai muka tura su a asusun banki daban daban, ciki harda na gwamna Fayose”

Alade ya kara da cewa Agbele ya umarci da mu aika miliyan N263 zuwa Ado Ekiti. Nan dai aka daga sauraron karar zuwa ranakun 25, 26 da 27 na watan Janairun 2017.

The post Bahallatsar $2.1b: Shaidu sun saka Fayose cikin tsaka mai wuya appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Originally posted by Adeshola
Share on Google Plus

About Unknown

This is a short description in the author block about the author. You edit it by entering text in the "Biographical Info" field in the user admin panel.