– A karon farko Hillary Clinton ta fito fili ta bayyana irin takaicinta a kan shan kayen da ta yi a hannun Donald Trump a zaben kasar da aka yi a makon jiya.
– Misis Clinton ta ce sai da ta ji kamar ta hada kanta da gwiwarta ta rufe a cikin wani “littafi sannan na ki fitowa daga gida har abada.”
Hillary Clinton
Sai dai a wani jawabi da ta yi a wurin wata gidauniyar yara marasa galihu, Misis Clinton ta yi kira ga mahalarta taron da su zage dantse domin yaki wajen kare martabar muradun Amurka kuma kada su taba karaya.
‘Yar takarar jam’iyyar Democrat din dai ita ce ta lashe yawancin kuri’un da aka kada a zaben, sai dai Mista Trump ya fi ta yawan wakilan da suke zabar shugaban kasar, abin da ya sa ya yi nasara.
KU KARANTA: Zamu sa kafar wando daya da Buhari idan – NUPENG
Misis Clinton ta shaida wa mahalarta taron cewa: “A gaskiya zan fada muku cewa ba na yi kokari sosai kafin na iya zuwa nan. Na san yawancin ku ba ku ji dadin sakamakon zaben ba. Ni ma ban ji ba, fiye da yadda kuke tsammani.
“Na san hakan na da matukar wuya. Na san cewa mutane da dama sun kashe tsawon wannan mako suna tambayar cewa anya wannan ita ce kasar Amurkan da muke tunani.”
Mahalarta taron sun yi ta jinjina mata, suna masu cewa gwiwoyinsu ba su yi sanyi ba.
A wani labarin kuma, Shugaba Shinzo Abe na Japan ya gana da zababben shugaban Amurka Donald Trump, domin tattaunawa tare da fayyacewa kasar sa kalaman da Mista Trump ya yi amfani da su a lokacin yakin neman zabe.
Daga bisani bayan tattaunawar da shugabannin biyu suka shafe tsahon mintina casa’in, wadda aka yi ta a dogon ginin Trump Towers da ke Manhattan.
Shugaba Abe ya shaidawa manema labarai cewa tattaunawar da suka yi da Mista trump ta kara masa karfin gwiwa, kuma a shirye kasar sa ta ke dan kulla dangantaka mai dorewa tsakanin ta da Amurka.
Japan dai ta nuna damuwa matuka a lokacin da aka sanar da Mista Trump a matsayin sabon shugaban Amurka, saboda rashin sanin tabbas din ko kasashen biyu za su ci gaba da kasancewa kawaye musamman da fuskar huldar diplomasiyya da tsaro.
A lokacin da yake yakin neman zabe, mista Trump ya ce dole kasashe kawayen Amurka su shiga cikin taimakon da Amurka ke badawa, da suka hada da biyan dakarun kawance na NATO maimakon ita kadai ta dauki nauyin su.
A kuma wannan lokacin ya ce kamata ya yi Japan ta samar da makamin nukiliya na kashin kan ta, da kuma duba yiwuwar ci gaban kasashen biyu ta fuskar kasuwanci.
A ranar 20 ga watan junairu ne Mista Trump zai sha rantsuwar kama aiki, a kuma wannan ranar ne wa’adin mulkin shugaba Barack Obama ke zuwa karshe.
The post Kalaman Clinton a karon farko bayan zaben Amurka zai baka mamaki (Karanta) appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.
Originally posted by Adeshola