Breaking News
Loading...

Jama’a sun yi tir da halayyyar ‘yan Lagos bisa wannan dalili

Jama’a sun yi tir da halayyyar ‘yan Lagos bisa wannan dalili

Jama’a sun yi tir tare da nuna bakin ciki matuka dangane da rahotani tare da wasu hotuna na wani yaro dan shekara 7 da aka kone kurmus a Lagos a bisa zargin sata

mercy

‘Yan wasan finafinan Nollywood da su ma sun nuna takaicinsu na kone yaron da aka ce ya saci garin kwaki

 

Jama’a sun bayyana ra’yoyinsu na bacin rai dangane da kisan wani yaro da a ka yi a Lag0s ta hanyar kone shi kurmus a bisa zargin satar garin kwaki.

wasu jaruman shirin finafinan turanci da ake yi a kudancin kasar Mercy Johnson da kuma Anne Idibia na daga cikin mutane da suka magantu kan lamarin mai sosa zuciya na rashin imani.

A sanarwar da ta lika a shafinta na sada zumunta da tafka muhawara, Annie Idibia na cewa, “wasu na cewa shekarunsa 7, wasu kuma 20… amma shin haka ya dace?, wannan hotoda na kalla ya san a kasa barci.. gaskiya ya kamata a kawo karshen wannan dabbanci da sunan hukunci, don hakan bai dace ba.”

KU KARANTA KUMA: An kona wani yaro karami da ran sa don ya saci garin Rogo

Ita kuwa Mercy a na sharhin cewa ta ke yi, “….ta yaya za ce hakan ta faru ga yara bayan sune mabudin aljanna, ta yaya za’a bari hakan ta faru ga yara, kuma mu ce muna son baki  su zo su zuba jari a kasarmu? Wane irin sako muke isarawa duniya? Ni dai bana goyon bayan wannan aika-aika, da na kowa ne.”

Rundunar  ‘yan sandan jihar Legas ta musanta rahotannin da kuma hotunan bidiyon yaron da aka kone kurmus saboda ya saci gari, kuma ake ta yadawa a shafukan intanet.

A cewar majiya, kwamishinan ‘yan sandan jihar Fatai Owoseni ne ya karyata labarin duk da cewa ga hotunan na bidiyo na duka da kuma kone yaron kurmus.

Jama’a dai sun fusata tare da neman da lallai ‘yan sandan su gudanar da bincike tare da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Ku biyomu a shafin Tuwita a @naijcomhausa

The post Jama’a sun yi tir da halayyyar ‘yan Lagos bisa wannan dalili appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Originally posted by Adeshola
Share on Google Plus

About Unknown

This is a short description in the author block about the author. You edit it by entering text in the "Biographical Info" field in the user admin panel.