Breaking News
Loading...

Kamar Ebola? Wani zazzafan zazzabi ya kashe mutum 32 a Niger

Kamar Ebola? Wani zazzafan zazzabi ya kashe mutum 32 a Niger

– Akalla mutum 32 sun mutu tun watan Agusta sakamakon zazzabin Rift Valley a Niger kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya rawaito ma’aikatar lafiyar kasar na cewa.

– A wata sanarwa da ma’aikatar lafiya ta fitar, ta ce annobar ta bazu a yankin Tahoua, inda mutum 230 suka kamu da ita.

Lassa fever is carried by rats and the diseases has now spread to six states in Nigeria.

Lassa fever is carried by rats and the diseases has now spread to six states in Nigeria.

Zazzabin Rift Valley dai cuta ce da sauro ke yadawa – hasali ma dai cutar dabbobi ce kamar awaki, akuyoyi da kuma rakuma.

KU KARANTAKamfanin Glo na cikin tsaka mai wuya saboda

Sai dai makiyaya da masu kula da dabobbi suna da hadarin kamuwa da cutar kamar saboda zai iya yaduwa ta hanyar taba jinin dabba ko kuma idan sauron da ya kuma da cutar ya cije mutum.

Alamomin cutar na farko da ke bayyana a jikin mutum sun hada da zazzabi da ciwon kai wanda zai iya tsananta zuwa fitar da jini daga dadashi da hanci a wasu lokutan ma mutum ya shiga halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ce yawan mace macen da ake yi ya ragu da kashi 50 cikin 100 a cikin watanni uku da suka wuce zuwa kashi 14 cikin 100, sakamakon wani shirin wayar da kan jama’a na gwamanti, da ya bukaci mutane su rika birne gawarwakin dabbobi tare da yin takatsantsan wurin mu’amala da matattun dabbobi da kuma gujewa shan madara wadda ba a gauraya ba.

A wani labarin kuma makamancin wannan, Hukumomin kula da lafiya a Jamhuriyar Nijar sun ce wata baƙuwar cuta da ta bulla a yankin Tahoa ta kashe mutum akalla 21.

Cutar, wadda ake dauka daga jikin dabbobi, ta bulla ne a ‘yan kwanakin da suka gabata.

Wasu jami’an ma’aikatar lafiya ta kasar sun shaida wa majiyar mu cewa ana iya daukar cutar ta hanyar shan nonon dabbar da ke dauke da ita.

Sun kara da cewa suna daukar matakai domin shawo kan wannan cuta da ke saurin yaduwa.

The post Kamar Ebola? Wani zazzafan zazzabi ya kashe mutum 32 a Niger appeared first on Nigeria News today & Breaking news | Read Naij.com 24/7.


Originally posted by Adeshola
Share on Google Plus

About Unknown

This is a short description in the author block about the author. You edit it by entering text in the "Biographical Info" field in the user admin panel.